Home Labaru Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Da Ya Taba Kwace...

Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Da Ya Taba Kwace Bindigar DSP

415
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra, ta ce ta samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami Chinedu Ani, wanda ya taba yi wa wani babban jami’in dan sanda mai mukamin DSP fashi a kauyen Idodo da ke kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki tare da kwace ma shi bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sada na jihar DSP Haruna Mohammed, ya ce ‘yan sandan rundunar SARS sun samu nasarar kama Ani ne da misalin karfe 11:00 na safiyar Asabar da ta gabata, a wata moboyar su da ke Obosi a karamar hukumar Idemili ta Kudu da ke jihar Anambra.

Kakakin ya kara da cewa, dan shekaru 28 a duniya, Chinedu Ani dan asalin karamar hukumar Nkana ta Gabas ne da ke jihar Enugu.

Ya ce bayan ya sha matsa a ofishin ‘yan sanda, mai laifin ya jagoranci rundunar ‘yan sanda zuwa kauyen Ezeama da ke karamar hukumar Nkana ta Arewa a jihar Enugu, inda ya boye bindigar DSP Ogalagu.

Leave a Reply