Home Labaru Wata Sabuwa: Barayi Sun Yi Wa Sakateriyar Jam’iyyar APC Karkaf A Jihar...

Wata Sabuwa: Barayi Sun Yi Wa Sakateriyar Jam’iyyar APC Karkaf A Jihar Ogun

317
0

Wasu da ba a san ko su wanene ba, sun barke sakareriyar jam’iyyar APC ta jihar Ogun, su ka sace takardun muhimman bayanai tare da sace kayayyakin da ke cikin sakateriyar.

Baya ga satar kayayyakin da su ka yi masu tarin yawa, barayin sun kuma lalata wasu sassa na sakateriyar, domin hatta rufin ofisohin sai da su ka yi ma shi kaca-kaca.

Kayayyakin da aka lalata aka kuma sace wasu sun hada da takardun muhimman bayanai, da na’urorin sanyaya daki da akwatunan talbijin na ilahirin ofisoshin, da kuma kujeru da dama.

Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Ogun Derin Adebiyi ya sanar da haka, a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Ya ce duk da dai ba a san dalilin da ya sa aka fasa sakateriyar ba, amma akwai zargin wani abu a kasa, domin saura makonni biyu kacal wa’adin gwamna Adekunle Amosun ya kare.

Leave a Reply