Hukumar yaki da ayyukan da su ka jibanci bada cin hanci da karbar rashawa a Madagascar, ta mika wa kotu sunayen wasu daga cikin ‘yan Majalisar kasar da su ka karbi nagoro makonni biyu kafi a je zaben ‘yan majalisun kasar.
Hukumar, wadda ta kwashe kusan tsawon shekara daya ta na bincike, ta zakulo sunayen ‘yan majalisu 79 da ake sa ran kotu za ta yi aikin ta a kai.
Jam’iyyun adawa dai su na zargin wasu daga cikin ‘yan majalisun da karbar kusan milyan 50 na kudin kasar.
A lokacin karbar rantsuwar soma aiki, Shugaban kasar ya dauki alkawalin yaki da cin hanci da rashawa.
You must log in to post a comment.