Home Labaru Tsaro: ‘Yan Najeriya Na Cikin Matsala — Shugaban Jami’ar Al-Hikmah

Tsaro: ‘Yan Najeriya Na Cikin Matsala — Shugaban Jami’ar Al-Hikmah

184
0

Shugaban jami’ar Al-Hikmah, dake Ilorina jihar Kwara, Farfesa
Noah Yusuf, ya ce kisan da aka yi wa manoma, hadari ne ga
samun isasshen kayan abinci.

Farfesa Noah Yusuf, ya ce bayan wannan kashe-kashe, za a ga
tasirin ambaliyar ruwa da aka samu a wasu jihohi da kuma
rikicin makiyaya da manoma da ake yi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da manema
labarai a wajen shirin bikin yaye wasu daliban da suka kammala
karatu. garin a jami’ar.

Shugaban jami’ar ta Al-Hikmah ya ce a shekarar nan za ayi
bikin yaye dalibai ta kafar yanar gizo saboda annobar COVID-
19 da ta takaita cakuduwar jama’a.

Ya ce wadannan abubuwa za su yi sanadiyyar jawo ci-baya ga
nasarar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta
samu a harkar noma.

Hakan na zuwa ne bayan an samu ‘yan ta’addan Boko Haram
sun kashe wasu manoma fiye da 40 a kauyen Zabarmari, dake
karamar hukumar Jere a jihar Borno.