Home Labaru Rashin Tsaro: Bola Tinubu Ya Bada Shawarar Yadda Za A Kawo Karshen...

Rashin Tsaro: Bola Tinubu Ya Bada Shawarar Yadda Za A Kawo Karshen Matsalar

193
0

Jigo kuma mai fada aji a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu
ya ce wajibi ne a hada karfi da karfe idan ana son kawo karshen
rashin tsaro a Najeriya.

Tinubu, ya bayyana irin kidimewa da gigicewar da ya yi bayan
da ya sami labarin yadda kungiyar Boko Haram suka yi wa
manoma a jihar Borno kisan wulakanci.

Sannan kuma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar
Borno, Babagana Zulum, da daukacin al’umar jihar a kan kisan
manoma 43 na Zabarmari dake karamar hukumar Jere a jihar.

Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewar manoman da ba su ji ba
basu gani ba, sun mayar da hankulansu wurin nema wa iyalansu
abinci, amma rashin tsaro ya janyo musu bala’i.