Home Labaru Harin Zabarmari: Sarkin Musulmi Ya Nuna Damuwa Kan Halin Da Tsaro A...

Harin Zabarmari: Sarkin Musulmi Ya Nuna Damuwa Kan Halin Da Tsaro A Najeriya

224
0
Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad II
Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad II

Mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III
ya bayyana damuwa kan yadda ‘yan bindiga ke rike da ikon
yankuna da dama, bayan hare-haren baya-bayan nan ciki har da
Zabarmari wanda da Boko Haram su hallaka manoman
shinkafa.

Cikin kalaman Sarkin na Musulmi wanda ke kunshe a wata
sanarwa da kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta fitar ya ce, yanzu
haka ‘yan-bindigan na shinfida wa al’umma wasu ka’idojin da
suka zama dole su mutuntasu kafin ba su damar ci gaba da
al’amuransu na yau da kullum.

Al’amuran tsaro na ci gaba da tabarbarewa a Najeriyar
musamman yankin Arewaci inda ko a farkon makon nan
mayakan kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga IS wato
ISWAP suka sace wani ma’aikacin jin-kai da wasu jami’ai biyu
a arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni sun ce an sace mutanen ne a wani shingen ababen
hawa da ke kauyen Wakilti na jihar Borno.