Home Labaru Tsaro: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Dakarun Chadi 100 A Yakin Tafkin...

Tsaro: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Dakarun Chadi 100 A Yakin Tafkin Chadi

869
0
Tsaro: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Dakarun Chadi 100 A Yakin Tafkin Chadi
Tsaro: ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Dakarun Chadi 100 A Yakin Tafkin Chadi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa za ta dauki tsauraran matakai domin ganin bayan kungiyar mayakan Boko Haram.

Buhari ya sanar da haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a fadar da ke Abuja.

Ganawar dai na zuwa ne jim kadan bayan mayakan Boko Haram sun hallaka dakarun sojin kasar Chadi 100 a yankin tafkin Chadi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, ya zama dole gwamnatin sa ta dauki matakan tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankunan da Boko Haram suka yada zango a Nijeriya.

Gwamna Zulum ya bayyna kisan da sojojin Chadin su ka yi wa ‘yan ta’adda zai iya kawo barazana ga harkokin tsaron Nijeriya.

Shugaba Buhari da gwamna zulum sun amince da cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen Boko Haram da sauran miyagun ayyuka da ke faruwa a yankin tafkin Chadi.