Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya koka bisa halin da asibitocin Nijeriya su ke ciki.
Boss Mustapha wanda shine shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar Coronavirus, ya ce ya gano irin mummunan halin da asibitocin Nijeriya su ke ciki ne bayan an zabe shi shugabancin kwamitin.
Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin wani taron da ya yi da shugabannin majalisar tarayya a ranar Alhamis din da ta gabata, tare da cewa annobar Coronavirus ta bada damar duba halin da asibitocin Nijeriya su ke ciki.
Haka kuma, ya ce an fara shirin gyara asibitocin tare da inganta su sakamakon barkewar annobar COVID-19 a Nijeriya, tare da cewa kwamitin da ya ke shugaban ta zai yi kokarin ganin sun tsara yadda za a yi gyara a bangaren kiwon lafiya.
Boss Mustapha ya kara da cewa, kwamitin sa zai aikin bisa gaskiya da rikon
amana, ta hanyar karbar gudumawa tare da mika sui dnda ya dace don yaki annobar
Coronavirus.
You must log in to post a comment.