Home Labaru COVID-19: An bude garin Wuhan

COVID-19: An bude garin Wuhan

530
0
An ba da izinin fita ga duk wanda ke da alamar kore a manhajar lafiyar da yawancin mazauna garin Wuhan ke amfani da ita.
An ba da izinin fita ga duk wanda ke da alamar kore a manhajar lafiyar da yawancin mazauna garin Wuhan ke amfani da ita.

Hukumominn kasar China sun bude garin Wuhan inda aka fara samun bullar cutar coronavirus, tun a watan Disamban shekarar 2019.

Akalla mutum 70,000 sun fice daga Wuhan a cikin ‘yan sa’o’i a ranar Laraba bayan janye dokar hana shiga da fita da aka sanya a birnin na tsawon kwana 76.

Gwmantin kasar China ta amince wa duk mazaunin Wuhan da manhajar kula da lafiya da ke cikin wayar hannunsa ta nuna alamar kore ya fita daga garin mai mazauna miliyan 10.

Yawan masu cutar coronavirus a kasar China na kara raguwa matuka yayin da masu kamuwa da ita a wasu kasashe ke kara yawa.

Daga bullar cutar zuwa yanzu mutum miliyan 1.4 suka kamu da ita, ciki har da mutum 300,000 da suka warke da wasu dubu 82 da ta yi ajalinsu.

Yanzu Amurka ce ta fi yawan masu cutar a duniya, inda mutum fiye da 400,000 suka kamu da ita.