Home Labaru Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Shanu 500 A Jihar...

Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Shanu 500 A Jihar Zamfara

295
0

Akalla Mutane 9 ne su ka jikkata, a wani samame da ‘yan bindiga su ka kai wani kauye da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari garin Wara-Wara da ke karamar hukumar Tsafe, inda su ka yi awon gaba da tarin dabbobi.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka wa garin ne a kan babura akalla 15, inda su ka kora akalla  dabbobi 500.

Sai dai Majiyar ta ce ba a samu asarar rayuka yayin harin ba, amma akalla mutane 9 sun jikkata yayin da su ke kokarin gudun tsira.