Akalla Mutane 9 ne su ka jikkata, a wani samame da ‘yan bindiga su ka kai wani kauye da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce, wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari garin Wara-Wara da ke karamar hukumar Tsafe, inda su ka yi awon gaba da tarin dabbobi.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka wa garin ne a kan babura akalla 15, inda su ka kora akalla dabbobi 500.
Sai dai Majiyar ta ce ba a samu asarar rayuka yayin harin ba, amma akalla mutane 9 sun jikkata yayin da su ke kokarin gudun tsira.

