Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Za A Tsaurara Matakan Shiga Asibitin Aso Rock

Kiwon Lafiya: Za A Tsaurara Matakan Shiga Asibitin Aso Rock

338
0

Gwamnatin Tarayya za ta kara tsaurara matakan rage yawan mutanen da ke shiga asibitin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Babban sakataren fadar shugaban kasa Tijjani Umar ya bayyana haka, inda ya ce gwamnati ta yi hakan ne domin inganta ayyukan asibiti

Tijjani Umar, ya ce bisa ga yadda tsarin ya ke, kamata ya yi asibitin ya rika kula da kiwon lafiyar shugaban kasa da iyalen sa da mataimakin shugaban Kasa da iyalen sa da ma’aikatan fadar shugaban kasa.

A shekara ta 2015, gwamnati ta ware wa asibitin naira biliyan 3 da miliyan 94, sannan asibitin ya samu naira biliyan 3 da miliyan 87 a shekara ta 2016.

A shekara ta 2017 kuma gwamnati ta ware naira biliyan 331 da miliyan 70, sannan a shekara ta 2018 asibitin ya samu naira biliyan 1 da 300, yayin da a shekara ta 2019 ya samu naira miliyan 800.

Sakamakon haka ne, shugaba Muhammadu Buhari ya Sanar da Shirin da gwamnati ke yi wajen dawo da darajar da aka san asibitin da ita.