Home Home Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 7 Sun Sace Wasu Da...

Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 7 Sun Sace Wasu Da Dama A Ƴantumaki

86
0
Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 7 Sun Sace Wasu Da Dama A Ƴantumaki

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan kasuwa akalla 7, sun kuma yi garkuwa da wasu da dama a kasuwar ‘yan tumaki da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina.

Wani mazaunin garin Magaji Basiru ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun afka cikin kasuwar ne da rana tsaka a kan Babura su ka yi harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yayin guje-guje ne wasu yara biyu su ka rasa rayukan su.

Ya ce ‘yan bindigar, sun shiga ɓangaren masu saida wayoyin hannu kai tsaye, inda su ka kwashi wayoyi babu adadi, sannan sun sace mutane da dama baya ga waɗanda su ka kashe da kuma waɗanda su ka ji rauni.