Home Home Ta’addanci: Mutanen Da ‘Yan Bindiga Su Ka Kashe Da Rana Tsaka A...

Ta’addanci: Mutanen Da ‘Yan Bindiga Su Ka Kashe Da Rana Tsaka A Zamfara Sun Kai 17

42
0
‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17, a wasu hare-hare da su ka kai a kan kauyuka hudu da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda su ka yi awon gaba da dimbim dabbobi bayan sun yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka Kauyukan  Kadaddaba da Rafin Gero a karamar hukumar Anka, inda su ka tarwatsa al’umma ba tare da samun wani kalubale daga jami’an tsaro ba.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun shiga  kasuwar  Rafin Gero su ka yi awon gaba da dimbin shanu da rakumma da sauran dabbobi.

Mazuna yankin sun ce, duk da cewa mutane sun tsere cikin daji don neman tsira, amma ‘yan bindigar sun yi ta bin su a kan babura su na harbewa.