Home Home Tura Ta Kai Bango: Mun Ja Wa Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya Kunne...

Tura Ta Kai Bango: Mun Ja Wa Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya Kunne – Uba Sani

120
0
Dan majalisar dattawa Sanata Uba Sani, ya ce majalisar ta gargadi manyan hafsoshin tsaron Nijeriya tare da ja masu kunne su maida hankali wajen samar da tsaro a fadin Nijeriya, musamman yankin Arewa Maso Yamma.

Sanata Uba Sani, ya ce tabbas tura ta kai bango, domin ‘yan bindiga sun samu damar cin karen su ba babbaka saboda sakacin da aka samu a wasu sassan tsaron kasar nan.

Ya ce ya na daga cikin kiran da su ka yi wa manyan hafsoshin tsaron Nijeriya, su yi amfani da karfin soji domin kawo karshen matsalar tsaro musamman yankin Arewa Maso Yamma.

Uba Sani ya kara da cewa, majalisa na ware wa fannin tsaro makudan kudade domin su yi amfani da su, don haka dole su tunkari ‘yan ta’adda domin gamawa da su.

Leave a Reply