Dakarun Sojin Saman Operation LAFIYA DOLE Sun Kai Mumunan Hari Kan Yan Tada Kayar Bayan Boko Haram A Unguwar Alafa Dake Cikin Dajin Sambisa, Jihar Borno A Ranar Litinin, 10 Ga Watan Yuni, 2019.
Kakakin Hukumar Sojin Saman, Bimbo Daramola, Ya Bayyana Wannan Ne A Wani Jawabin Da Ya Saki Da Yammacin Yau Litinin, Yace: “Dakarun Sojin Sama Na Rundunar Operation Lafiya Dole Sun Samu Wani Nasara Kan Yan Ta’addan Boko Haram Dake Zaune A Dajin Sambisan Jihar Borno.”
“Harin Wanda Ya Kai Ga Ragargaza Babbar Cibiyar Taronsu Tare Da Hallaka Yan Ta’adda Da Dama, Ya Gudana Ne A Yau 10 Ga Yuni 2019, Bayan Bincikin Na’ura Ya Gano Wata Rumfa A Alafa Cikin Dajin Sambisa Inda Yan Ta’addan Ke Amfani Da Shi Wajen Baiwa Maharansu Umurni.”
Yayinda Jirgin Ya Gano Gidan Daga Sama, Ya Hangoshi Cike Da Yan Ta’addan A Cikin. Ba Tare Da Bata Lokaci Ya Sakar Musu Wutar Aradu Wanda Ya Ragargaza Cibiyar Tare Da Kisan Yan Ta’addan.”
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.














































