Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Bakuncin Wasu Wakilan Gwamnatin Kasar Italiya Da Zasu Taimaka Wa Najeriya Kwato Kadarori Da Dukiyoyin Da ‘Yan Kasar Suka Saya Da Kudaden Cin Hanci A Kasashen Ketare.
A Sanarwar Da Garba Shehu, Kakakin Shugaban Kasa Ya Fitar, Ya Ce Buhari Ya Yi Maraba Da Yunkurin Gwamnatin Kasar Ta Italiya Na Taimakon Najeriya A Yakin Da Take Yi Da Cin Hanci Da Karya Tattalin Arzikin Kasa.
Wani Dan Najeriya Da Ya Kasance Bakin Mutum Na Farko Da Ya Taba Cin Zaben Dan Majalisa A Kasar Italiya Na Daga Cikin Tawagar Wakilan Da Suka Ziyarci Buhari, Kuma Zai Zauna A Gida Najeriya Domin Halartar Bukukuwan Bikin Zagayowar Ranar Dimokraddiya, 12 Ga Watan Yuni, Wanda Za A Yi Ranar Laraba.
Kazalika, Ya Taya Shugaba Buhari Murnar Sake Samun Nasarar Lashe Zaben Kujerar Shugaban Kasa A Karo Na Biyu, Kamar Yadda Garba Shehu Ya Wallafa A Shafinsa Na Tuwita.
Gwamnatin Buhari Ta Kwace Kadarori Masu Yawa Daga Hannun Tsofin Shugabanni Da Ma’aikatan Gwamnati Da Ake Tuhuma Da Cin Hanci.
Kazalika, Ta Aika Wasu Tsofin Gwamnoni Da Shugabannin Hukumomin Da Aka Samu Da Laifin Wawure Kudin Kasa Zuwa Gidan Yari.
A Kwanakin Baya Ne Shugaba Buhari Ya Bawa Ministar Kudinumarni Ta Hada Kai Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Karya Tattalin Arziki (EFCC) Domin Sayar Da Dukkan Kadarorin Da Akwa Kwace Daga Hannun Wadanda Aka Gurfanar A Kotu Bisa Tuhumar Su Da Cin Hanci.
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.