Dakarun Sojoji Uku Na Kasar Kamaru Da Mutane Da Dama Sun Riga Mu Gidan Gaskiya A Yayin Aukuwar Wani Mummunan Harin Dare Na ‘Yan Kungiyar Masu Tayar Da Kayar Baya Ta Boko Haram Kamar Yadda Rahotanni Suka Bayyana.
Hukumomin Tsaro A Ranar Litinin Da Ta Gabata Sun Bayyana Cewa, Kungiyar Masu Tayar Da Kayar Baya Ta Boko Haram Sun Yiwa Wani Sansanin Dakarun Soji Diban Karan Mahaukaciya Babu Zato Babu Tsammani A Gabar Tafkin Chadi.
Wannan Hari Da Ya Auku A Sansanin Dakarun Soji Dak Kauyen Darak A Yammacin Tafkin Chadi Cikin Kasar Kamaru, Ya Salwantar Da Rayukan Dakarun Soji Uku Da Kuma Farar Hula Da Dama Da Ba A San Adadin Su Ba.
Tun Kimanin Tsawon Shekaru Goma Da Daurar Damarar Ta’addanci, Kungiyar Boko Haram Ta Samwantar Da Rayukan Kimanin Mutane 27,000 Tare Da Raba Kimanin Mutane Miliyan 1.7 Da Mahallansu A Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Kawowa Yanzu Dakarun Sojoji Na Kasar Najeriya, Chadi, Kamaru Da Kuma Nijar, Sun Gaza Fatattakar Wannan Miyagun ‘Yan Ta’adda Da Suka Zamto Alakakai Wajen Ci Gaba Da Cin Karen Su Babu Babbaka Musamman A Gabar Tafkin Chadi.
Ana Iya Tuna Cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Lashi Takobi Kan Cewa Sabuwar Gwamnatin Sa A Wa’adin Ta Na Biyu, Ba Za Ta Rangwanta Wa Dukkanin Wasu ‘Yan Ta’adda Masu Tayar Da Zaune A Kasar Nan.
Shugaban Kasa Buhari Yayin Halartar Taron Kungiyar Kasashen Yankin Tafkin Chadi Da Aka Gudanar Makonni Biyu Da Suka Gabata, Ya Ce Lokaci Ya Karato Da Ya Kamata A Gaggauta Kawo Karshen Ta’addancin Boko Haram
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.