Home Labaru Ta’addanci: Batagarin Matasa Sun Fara Rushe Wani Masallaci A Jihar Delta

Ta’addanci: Batagarin Matasa Sun Fara Rushe Wani Masallaci A Jihar Delta

298
0

Wasu batagarin matasa sun rushe wani bangare na wani masallaci da ake ganawa a wata unguwa mai suna Kiagbodo mahaifar tsohon Minista, Cif Edwin Clark a jihar Delta.

Shugaban karamar hukumar Burutu dake yankin ya sanar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, sannan aka dakatar da matasan daga rushe masallacin gaba daya a unguwar.

Matasan sun fara rushe masallacin ne bayan Mallam Abubakar Kore-keme, mutumin dake gina Masallacin a gidansa dake Kiagbodo ya yi burus da gargadin da suka rika yi masa akan basa son a gina musu Masallaci a unguwa.

Mallam Kore-keme, ya ce matasan sun zo sun rushe Masallacin ne bisa umarnin wani fitaccen mutum dan asalin unguwar, inda ya  lashi takobin cewa babu wani abu da zai firgita shi har ya fasa gina Masallacin a cikin gidansa.

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa lokacin da yake magana da yan jarida

Sai dai Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya kira shugaban karamar hukumar domin ya sami cikakken bayani a kan abinda ya faru.

Leave a Reply