Home Labaru Tsaro: Shugaban Tsaro Ya Yi Jawabi A Kan Garkuwa Da Magajin Garin...

Tsaro: Shugaban Tsaro Ya Yi Jawabi A Kan Garkuwa Da Magajin Garin Daura

628
0

Tsawon kwanaki tara kenan, bayan an garkuwa da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba har yau ba a sako shi ba.

An dai yi garkuwa da Magajin Garin Daura ne a ranar 1 ga watan Mayu a gidan sa da ke garin Daura, amma rahotanni sun ce har ya na hannun wadanda su ka yi garkuwa da shi.

A karshen tattaunawar da shugaba Buhari ya yi da su a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shuwagabannin hukumomin tsaro sun ce an kama wasu da ke da hannu a lamarin.

Babban hafsan sojin ruwa Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas, ya ce ana ci-gaba da kokari sosai, sannan an kama manyan wadanda ake zargi da hannu a lamarin, kuma akwai tabbacin cewa nan da dan lokaci kadan za a gurfanar da wadanda ke da alhakin lamarin.

Ibas, ya ce an yi tattaunawa ta sa’o’i hudu domin yi wa shugaban kasa jawabi game da lamarin tsaro bayan dawowar sa daga kasar waje.

A halin da ake ciki, wata majiya mai kusanci da iyalan magajin garin Daura, ta ce har yanzu ba su ji wani kwakkwaran bayani a kan kokarin da ake yi domin kubutar da shi.

Leave a Reply