Akalla malaman addinin Musulunci hudu ne su ka sanar da yin murabus daga gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.
Malaman da su ka yi murabus kuwa sun hada da shugaban hukumar Hisbah Aminu Daurawa, da Shugaban hukumar mahajatta ta jihar Kano Abba Koki, da Kwamishinan hukumar gudanar da Shari’a na 1, Ababukar Kandahar, da Kwamishinan hukumar Zakkah da Hubsi na II Nazifi Inuwa.
Dukkan malaman hudu dai sun gabatar da wasikun ajiye aiki ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu na shekara ta 2019.
Sheikh Daurawa, wanda ya kasance daya daga cikin malaman da su ka yi Allah wadai da bidiyon cin hancin Ganduje a hudubar sa ta ranar Juma’a, ya ce ya yi murabus ne a kan wasu dalilai na kashin kan sa.
You must log in to post a comment.