Rahotanni daga jihar Kano na cewa, jami’an fadar masarautar Kano sun soma gurfana a gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano, domin bada ba’asi a kan yadda fadar ta kashe kudaden ta tun daga shekara ta 2013 zuwa yau.
Wannan matakin dai ya kara fito da tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar Kano.
A farkon makon nan ne gwamnatin jihar Kano ta aika wa masarautar wasikar gayyatar wasu jami’an ta, a ci-gaba da binciken yadda fadar ta kashe kudaden ta.
Wannan dai ya na zuwa ne, kwana guda bayan gwamnatin Kano ta tabbatar da dokar kara yawan masarautu a jihar.