Home Labaru Tsaro: Rundunar ‘Yan Sandan Plateau Ta Mutane 26 Da Aikata Miyagun Laifuka

Tsaro: Rundunar ‘Yan Sandan Plateau Ta Mutane 26 Da Aikata Miyagun Laifuka

181
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da yin kudaden jabu da fashi da makami da satar ababen hawa  da shiga kungiyar asiri da dai sauran su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Plateau CP Isaac Akinmoyede lokacin da yake magana da yan jarida

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Isaac Akinmoyede ya gurfanar da mutane a hedkwatar rundunar da ke Jos, tare da bayyana irin laifuffukan da suka aikata, inda ya kara da cewa za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike a kan su.

Isaac Akinmoyede ya ce sun kuma kwace makamai da alburusai a hannun batagarin, sannan ya bukaci al’ummar jihar su rika lura yadda al’amura ke gudana a lungu da sako da ke fadin jihar  musamman a wannan lokaci da ake shiga karshen shekara.

Kwamishinan ya kuma yi alkawarin cewa, hukumar su ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kakkabe miyagun ayyuka a fadin jihar.