Home Labaru Ilimi: Hukumar SUBEB Ta Gano Sunayen Matattu 256 Da Ake Biyan Su...

Ilimi: Hukumar SUBEB Ta Gano Sunayen Matattu 256 Da Ake Biyan Su Albashi A Jihar Benue

319
0

Hukumar da ke kula da makarantun firamare a jihar Benue ta ce a shirinta na yin tankade da rairaya ta gano sunayen matattun malamai 256 da har yanzu su ke cikin jerin masu karban albashi.

Shugaban hukumar Mathew Mnyam ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Makurdi, inda ya kara da cewa daga yanzu za a cire sunayen matattun daga cikin masu karban albashin.

Mnyam ya kuma ce, hukumar za ta tura daraktoci hudu hutun dole na watanni uku domin ba hukumar damar duba lamura da dama cikin tsanaki.

Hukumar ta kuma  dakatar da wani ma’aikaci da ke da alhakin kula da sunayen da aka kama tare da wani ma’aikaci da aka yiwa sauyin wajen aiki a hukumar, bayan ya kasa jawabin aikin da aka bashi.

Mnyam ya yi barazanar cewa, bada dadewa ba hukumar za ta bi ta kan wasu manyan sakatarorin kananan hukumomi da basa kokari, sannan ya gargadi shugabannin makarantun da ke karban kudade daga hannun iyayen su janye daga hakan ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Leave a Reply