Home Labaru Ilimi Takardun Makaranta: Lai Muhammad Ya Ba ‘Yan Nijeriya Hakuri A Kan Takardun...

Takardun Makaranta: Lai Muhammad Ya Ba ‘Yan Nijeriya Hakuri A Kan Takardun Buhari

587
0

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya roki ‘yan Nijeriya su yafewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan batar da takardun makarantar sa na sakandare da ya yi.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad

Ministan ya bayyana haka ne a cikin wani shiri da aka gudanar da shi a gidan talabijin na Channels.

 Lai Muhammad ya bada hakurin ne bayan an yi masa tambaya a a kan da takardun makarantar shugaban Buhari, inda ya ce shugaban ya cancanci a yafe masa, saboda yanzu shekaru 53 kenan da ya kammala makarantar sakandare, sannan kuma bai ma san inda ya ajiye takardun na shi ba.

Ban hakurin na zuwa ne, bayan cece-kuce da ake ta yi a kan cewa, shugaba Buhari bai kammala karatun sa na sakandare ba.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne tsohon na hannun damar shugaba Buhari injiniya Buba Galadima ya caccaki shugaban kasa Muhammadu  Buhari akan cewa bashi da takardun makaranta.