Home Labaru Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wanda Ya Kashe Mata Da Mijinta...

Tsaro: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wanda Ya Kashe Mata Da Mijinta A Kano

191
0

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Salisu Idris dan shekaru 25 da aka ce ya bankawa wani gida wuta, wanda hakan ya yi  sanadiyar mutuwar mutane uku.

Mai magana da yawun rundunar ‘’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama wanda ake zargin, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a kauyen Gayawa tsohuwa da ke karamar hukumar Ungogo na jihar.

Kakakin ya ce tashin gobarar ta hallaka mata da mijin da dkuma diyar su guda, wanda hakan ya sa suka dauki alkawarin gudanar da bincike a kan lamarin.

A nashi bangaran kwamishinan ‘yan sanda jihar ya yi kira ga dukkan jami’an sashin binciken kwakwaf baza komar domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan aika-aika.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, inda ya kara da cewa an dauki hayan sa ne ta hanyar bashi naira dubu dari 2 domin ya kona wannan gida.