Home Labaru Cin Zarafin Pantami: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Jiga-Jigan PDP 3 Don...

Cin Zarafin Pantami: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Jiga-Jigan PDP 3 Don Amsa Tambayoyi

649
0

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gayyaci wasu jami’an jam’iyyar PDP sakamakon harin da aka yi ikirarin cewa wasu ‘yan ‘Kwankwasiyya sun kaiwa ministan sadarwa Isa Ali Pantami a filin tashin jiragen Kano na Aminu Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana haka ga maneam labarai a kano.

Kiyawa ya sun gayyaci wasu jiga-jigan PDP ciki har da shugaban jam’iyyar, Alhaji Rabi’u Bichi da direktan yakin neman zaben PDP a zaben  shekara ta 2019.

Da ya ke tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP a kano Malam Sanusi Bature Dawakintofa, ya ce wadanda ke tsaron ministan ne ba su yi aikin su yadda ya kamata ba.

A karshe ya ce ba ‘yan kungiyar Kwankwasiyya ba ne suka kai harin, domin jagoran tafiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi ‘ya’yan kungiyar su kasance masu biyaya ga doka a da oda.