Home Labaru Babu Wani Shiri Na Tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

Babu Wani Shiri Na Tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

273
0
Babu Wani Shiri Da Ake Yi Na Tsige Sarki Sanusi - Gwamnatin Kano
Babu Wani Shiri Da Ake Yi Na Tsige Sarki Sanusi - Gwamnatin Kano

Wata kungiya da ke Kano mai suna ‘The Renaissance Coalition’ a Turance, ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta na shirye-shiyen maida Sarkin Kano Muhammad Sanusi II zuwa masarautar Bichi.

Karanta Wannan: Ba-Zata: Gwamna Ganduje Ya Yi Sallar Idi Bayan Sarki Sanusi A Kano

Sai dai babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya yi watsi da ikirarin, cewa babu wani abu makamancin haka ta bangaren gwamnatin jihar Kano.

A baya dai mun ji cewa, dattawan jihar Kano a karkashin kungiyar sake farfado da martabar jihar Kano sun bankado wani sabon yunkuri da Ganduje ke yi na tsige mai martaba Sarkin Kano.

Wata majiya ta ce, tun bayan da gwaman jihar Kano ya kirkiri sabbin masarautu hudu a jihar tare da rage wa Sarki Sunusi karfin iko, aka lura Sarkin ya janye daga halartar tarurrukan gwamnatin jihar Kano.