Home Labaru Tsaro: Rundunar Soji Ta Mika Tubabbun Mayakan Boko Haram 151 Ga Gwamnatin...

Tsaro: Rundunar Soji Ta Mika Tubabbun Mayakan Boko Haram 151 Ga Gwamnatin Jihar Borno

713
0

Rundunar sojojin Najeriya ta mika tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 151 ga gwamnatin jihar Borno.

Shugaban rundunar hare-haren kwanton bauna Bamidele Shafa, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a  garin Bulunkutu wurin mika tubabbun mayakan bayan an kammala ba su horon sauya tunaninsu. 

Shugaban rundunar hare-haren kwanton bauna Bamidele Shafa

Shafa, ya ce  yanzu tubabbun mayakan za su iya koma wa cikin sauran jama’a, inda ya ce daga wadanda suka tuba su 151, akwai manya 132 da wasu masu karancin shekaru su 19, kuma dukkansu sun shafe tsawon makonni 52 a cibiyar kore zazzafar akida dake jihar Gombe.

Ya kara da cewa dukkanninsu  sun halarci dakunan bayar da ilimin addini da na zamani da kuma koya musu sana’o’i da warkar da su daga lahanin da miyagun kwayoyi suka yi wa kwakwalwarsu.

Ya ce rundunar hare-haren kwanton bauna shi ne ba mayakan kungiyar Boko Haram karfin gwuiwar ajiye makamnsu tare da ba su horo da taimako domin yi musu saiti kafin su koma su ci gaba da rayuwa a cikin sauran mutane.

Shafa, ya jinjinawa gwamnatin jihar Borno bi sa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an ba tubabbun mayakan horo domin koma su koma cikin al’umma.

Leave a Reply