Home Labaru Mutane 6 Sun Bace A Wani Harin Boko Haram A Borno

Mutane 6 Sun Bace A Wani Harin Boko Haram A Borno

244
0

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno sun bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari a kan ayarin motocin jami’an agajin da ke dauke da kayayyakin jinkai domin tallafa wa al’ummar jihar da rikici ya shafa.

Karanta Wannan: Matsalar Tsaro: Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki

A cikin wata sanarwa da kungiyar ACF mai rajin yaki da yunwa a yankunan da rikici ya daidaita, ta ce mayakan na Boko Haram sun hallaka direba guda da ke tuka motar da ke dauke da kayayyakin agajin, yayin da mutane 6 ciki har da jami’in agaji su ka bace.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta hannun babban jami’in da ke kula da ayyukan jinkai Edward Kallon, ta aike da sakon ganin hukumomin Nijeriyar sun yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mutanen 6 sun dawo da lafiyar su.