Home Labaru Wutar Lantarki: Buhari Ya Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniya Da Kasar Jamus

Wutar Lantarki: Buhari Ya Rattaba Hannu A Kan Yarjejeniya Da Kasar Jamus

1152
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci sa hannu a wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da wani kamfanin kasar Jamus mai suna Siemes domin inganta harkar samar da wutar lantarki a Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Mai  magan da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce an kulla yarjejeniyar ce a fadar shugaban kasa dake Abuja, inda ya ce yarjejeniyar za ta haifar da ‘Da mai ido.

Shugaba Buhari, ya ce burin gwamnatinsa shi ne inganta fanin wutar lantarki, kuma za inganta karfin gwiwar masu zuba jari, tare da samar da ayyuka da kuma rage tsadar gudanar da kasuwanci da kuma karfafa karin ci gaban tattalin arziki a Najeriya.

Ya ce shiyasa gwamnati ta bayar da umarnin cewar duk wasu kayayyaki da za’a yi a Najeriya su kasance masu inganci daidai da na Jamus da Ingila sannan akan kum akan farasi mai rahusa.