Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Soji Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro

Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Soji Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tsaro

225
0

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kara zage damtse wajen yakar ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram baki daya musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Sabon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole

Sabon kwamandan rundunar ta musamman dake yaki da ta’addancin kungiyar  da ake yiwa lakabi da Operation Lafiya Dole ya tabbatar da haka a wajen birne gawarwakin wasu jami’an soji 5 da suka rasa rayukansu a jihar Borno.

Ya ce akwai shirye-shirye da aka samar wajen tabbatar da cewa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu basu sha wahala wajen kula da jin dadinsu ba.