Home Labaru Karancin Albashi: Ma’aikatan Legas Sun Ce Ba Su Aminta Da Naira Dubu...

Karancin Albashi: Ma’aikatan Legas Sun Ce Ba Su Aminta Da Naira Dubu 30 Ba

217
0
Funmi Sessi, Shugabar Kungiyar Kwadago Ta Jihar Legas
Funmi Sessi, Shugabar Kungiyar Kwadago Ta Jihar Legas

A ranar Litinin da ta gabata ne, ma’akatan gwanatin a jihar Legas su ka ce ba za su karbi kasa da Naira dubu 50 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Kamar yadda shugabar kungiyar kwadago ta jihar Funmi Sessi ta sanar, ta ce su na bukatar sake sabon ciniki saboda ganin yadda jihar Legas take.

Ta ce ma’aikatan jihar Legas su na fuskantar wahalhalu da yawa kafin su kai wuraren aiki, don haka ba za su aminta da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Sessi ta kara da cewa, ba a biyan ma’aikatan yadda ya dace, lamarin da ta ce ya kara janyo tabarbarewar al’amurra, ta na mai cewa, Legas gari ne na musamman, inda Sufuri da kudin haya da hadurran da ke kan tituna su ka bambanta da na sauran garuruwa.