Home Labaru Tsaro: Matsalar Na Ci Mun Tuwa A Kwarya-Buhari

Tsaro: Matsalar Na Ci Mun Tuwa A Kwarya-Buhari

297
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya na daya daga cikin shugabannin kasashen duniya da suke fama da rashin farin ciki a dunya.
Shugabn kasa Buhari ya bayanna hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya ce hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun kazanta a wasu yankunan Najeriya.
Ya ce babu yadda za a yi ya zama mai farin ciki a yayin da ‘yan bindiga ke kashe ‘yan Najeriya, ya tabbatar da cewar shi ma mutum ne, kuma ya san zafin da wadanda abin ya shafa da iyalansu ke ji.
Shugaban kasa Muhammdu Buhari, ya sha suka a ‘yan kwanakin nan, saboda hare-haren da ake kai wa a Zamfara, da wasu jahohin Najeriya.
Sannan kuma Buhari ya sha suka, bayan da aka zarge shi da yin jaje kan kisan wani matashi a jihar Legas, ba tare da ya yi hakan ba kan kisan da ya faru a Zamfara a baya-baya nan.
Saboda kashe-kashen ne aka gudanar da zanga zanga a wasu sassan arewacin Najeriya domin jan hankalin gwamnati ta dauki.
Malam Garba Shehu, ya ce yadda ake saka siyasa a cikin irin wannan mummunan yanayi, ya nuna yadda siyasarmu take cikin hali na rashin ci gaba.