Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yanzun haka yake kasar Jordan zai wuce hadiddiyar daular Labarawa kafin ya dawo Najeriya.
Muhammadu Buhari zai bar birnin Amman dake kasar Jordan a yau ne, domin halartan wancan taron, inda ake sa ran zai gana da manyan shugabannin hadiddiyar daular Labarawa .
Rahotanni su tabbatar da cewar Sarkin Dubai kuma Firayim Minista na kasar, Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum, ne ya gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa taron da aka shirya a cikin kasar sa.
Taron da shugabannin za su gudanar zai mayar da hankali ne akan harkar bunkasa tattalin arzikin kasashe ta hanyar shigowar hannun jari.
Shugaban kasa Buhari ya na cikin manyan baki da za su yi magana wajen taron, wanda hakan zai ba Najeriya damar yin magana a gaban manyan kamfanoni na kasashe 140 da watakilai za su yi sha’awar shigowa Najeriya.
Rahoton ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari ya gana da Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed Bin Rachid akan wasu ‘Yan Najeriya da aka kama bayan sun yi wani fashi da makami a kasar.
You must log in to post a comment.