Wasu ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane sun gamu da ajalin su, yayin da jami’an ‘yan sanda su ka salwantar da rayukan su a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar dai ta kaddamar da wani shiri tare da hadin gwiwar ‘yan sintiri daga kauyen Kungana a karamar Bali kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Da ya ke tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin ta wayar tarho, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP David Misal, ya ce masu garkuwa da mutanen sun gamu da ajalin su ne yayin da jami’an tsaro su ka tarwatsa wani sansanin su da ke saman dutse.
DSP David Misal ya kuma bada shaidar cewa, an samu nasarar kama miyagun makamai da su ka hada da bindigogi da sauran kayan yaki daban-daban a sansanin na ‘yan ta’addan.
Ta’addancin
masu garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda masu satar mutane ke
kai wa baki ‘yan kasashen waje da ‘yan Nijeriya hari musamman masu idanu da
tozali.