Home Labaru Zaben 2023: Buhari Ya Ce Ba Zai Goyawa Kowa Baya Ba

Zaben 2023: Buhari Ya Ce Ba Zai Goyawa Kowa Baya Ba

314
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce bashi da wani shiri na kafa wani a matsayin dan takaran shi a zaben shuagabn kasa na shekarar 2023.

Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne da yake maida bayani kan bukatar da tawagar ‘ya’yan kungiyar progressives in academics, suka mika masa a lokacin da suka kai masa wata ziyara a fadar sa dake birnin Abuja.

Shugaban tawagar Bolariwa Bolajim, ya ce kungiyar su ta yi farin cikin ganin yadda Shugba Buhari ya sake dawo wa a karo na biyu, kuma da zarar ya kammala yana bukatar komawa gida ya hutu dan haka ya zama wajibi ya fidda wanda zai gaje shi.

Karanta Labaru Masu Alaka: Kungiyar Kwadago Ta Gargadi Shugaba Buhari A Kan Chris Ngige

Kungiyar tace tana bukatar ganin ya kawo wani kwararren matashi dake da burin ya shugabanci Najeriya ta yadda zai rika sanya shi a hanya wanda da zaran ya kamma yasan akwai wanda zai dora.

Sai dai shugaban kasa yace ba zai taba bayyana wani a matsayin wanda yake son ya gaje shi ba domin kar ya sa shi cikin matsala Ya ce ya gwammace ya gwsammace ya ja bakin shi ya yi shiru, duk wani mai nema shima ya yi gwagwarmaya kamar yadda ya yi domin kowa ya sani sau uku ya tsaya takara yana ci ana dannewa sai a karo na hudu Allah ya sa ya yi nasara.