Yayin da majalisar dattawa ta ke tantance shi, tsohon ministan wutar lantakrki, ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, ya ce ma’aikatun da ya jagoranta sun dawo da kimanin sundukai 720 da aka watsar dauke da kayayyakin wuta a lokacin da ya karbi aiki a matsayin minista.
Sai dai Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa, ma’aikatun sun yi wa Fashola yawa shi kadai, inda ya ce shi ya sa a yanzu kan sa ya ke cike da furfura saboda aikin jagoranci ma’aikatu uku sun yi ma shi girma shi kadai.
A
na shi bangaren, Sanata Dino Melaye ya bayyana bacin ran sa, game da aikin
tantance sabbin ministocin da majalisar dattawa ke yi a yanzu, inda ya zargi
‘yan majalisar da cewa sun zama ‘yan amshin shata.
You must log in to post a comment.