Home Labaru Tsaro: Masu Garkuwa Da Masu Ibada A Coci Sun Bukaci Miliyan 3

Tsaro: Masu Garkuwa Da Masu Ibada A Coci Sun Bukaci Miliyan 3

140
0
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara
‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 9 A Zamfara

Wadanda suka yi garkuwa da mambobin cocin Living Faith da ke yankin Osara a Karamar Hukumar Adavi a Jihar Kogi sun bukaci a ba su miliyan uku a matsayin kudin fansa.

Wata majiya ta rawaito cewa maharan sun shiga cocin da ke kan titin Lokoja zuwa Okene har suka yi awon gaba da mutum uku daga cikin masu ibada a cocin.

Daya daga cikin iyalan wadanda aka sace ya bayyana cewa tun ranar Litinin din da ya gabata maharan suka kira waya suka bukaci miliyan daya a kan kowane mutum da suka sace.

Ya ce sun roki maharan a kan su rage kudin fansar, suka kuma bayyana musu cewa wadanda aka sace din masu karamin karfi ne duba da yadda suke shan wahala sakamakon halin da ake ciki a kasar nan.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da manema labarai sukayi masa ba don jin ta bakinsa game da lamarin.

Leave a Reply