Home Labaru Matsalar Ruwan Fanfo: Kauyuka A Jihar Yobe Sun Samu Sauki

Matsalar Ruwan Fanfo: Kauyuka A Jihar Yobe Sun Samu Sauki

45
0

Al’ummar wasu garuruwa a Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe da suka shafe shekaru suna fama da matsalar tsaftataccen ruwan sha, sun wayi gari cikin murna suna diban ruwa mai kyau a fanfo.

Garuruwan da suka hada da Ngeji da Gadaka da garin na Fika, sun samu ruwan ne a lokacin da Sanata mai wakiltar Kudancin Yobe, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai, ya musu dalilin samun tallafin ta hanyar kai kokensu gaban Majalisar Zartarwa ta Kasa.

Majalisar Zartarwa ta amince da a samar da ruwan shan a yankunan karkarar da suka share shekara da shekaru suna rayuwa babu ruwan sha.

Aikin ya samar wa wadannan yankunan karkara tsaftataccen ruwan sha a karon farko, wanda kuma zai taimaka musu wajen ayyukansu na yau da kullum.