Home Labaru Tsaro: Makarantar NDA Ta Tabbatar Da Harin Da Aka Kai Mata A...

Tsaro: Makarantar NDA Ta Tabbatar Da Harin Da Aka Kai Mata A Kaduna

44
0
NDA

Makarantar horar da Sojojin Nijeriya NDA, ta tabbatar da kisan jami’an ta biyu yayin da ‘yan bindiga su ka kai hari a barikin su.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun sace wani jami’in soji, amma hukumar makarantar ta na kan bin diddigin ‘yan bindigar da su ka yi kutse a tsarin tsaron ta.

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Salau ya wallafa sanarwar kakakin rundunar sojin a shafin sa na Facebook, inda ya ce ‘yan bindiga sun yi kutse a tsarin tsaro na Kwalejin horar da sojojin Nijeriya da ke Kaduna.

Ya ce Makarantar tare da hadin gwiwar Babbar Runduna ta 1 ta Sojin Kasa da Rundunar Horar da dakarun Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro da ke Jihar Kaduna, su na bin sawun masu garkuwar a yankin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.