Home Labaru Jimami: An Dakatar Da Zaman Majalisar Zamfara Saboda Sace Mahaifin Kakakin Ta

Jimami: An Dakatar Da Zaman Majalisar Zamfara Saboda Sace Mahaifin Kakakin Ta

43
0
Zamfara-Assembly

Majalisar dokoki ta Jihar Zamfara, ta dakatar da zama har sai abin da hali ya yi sakamakon sace mahaifin kakakin majalisar da ‘yan bindiga su ka yi.

Makonni uku da su ka gabata ne, ‘yan bindiga su ka sace mahaifin kakakin majalisar Alhaji Mu’azu Abubakar, wanda shi ne hakimin Sabon Garin Magarya, tare da kishiyoyin mahaifiyar kakakin majalisar bayan sun kai hari garin.

Tuni dai an fara tattaunawa da ‘yan bindigar, inda rahotanni ke cewa maharan su na ta sauya sharrudan da su ke son a cika kafin su saki mahaifin kakakin majalisar.

Wata kwakwarar majiya ta shaida wa manema labarai cewa,  majalisar ta dakatar da zaman ta ne bayan afkuwar lamarin, inda wani babban jami’i a majalisar ya ce ‘yan majalisar sun damu matuka da afkuwar lamarin.