Home Labaru Rikicin Filato: Tekan Ta Bukaci Gwamnati Ta Biya Diyyar Wadanda Su Ka...

Rikicin Filato: Tekan Ta Bukaci Gwamnati Ta Biya Diyyar Wadanda Su Ka Rasa Rayukan Su

40
0
President Buhari & CAN

Kungiyar Kiristoci ta Tarayyan Eklesiyyoyin Kristi, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jiha su biya diyyar wadanda aka kashe a rikicin jihar Filato.

Shugaban kungiyar Rev. Moses Ebuga yayi wannan kiran, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a garin Jos.

Moses Ebuga, ya ce mutane da yawa sun rasa ‘yan’uwan su da dukiyoyin su, sannan da dama sun rasa gidajen su, don haka su ke bukatar tallafi.

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta biya diyyar ga iyalan wadanda su ka rasa rayukan su a rikicin kananan hukumomin Bokkos da Riyom da Bassa da Barkin Ladi.

Moses Ebuga ya kara da cewa, su na kira ga Hukumar bada Agajin Gaugawa ta Kasa da ta jihar Filato, su taimaka wajen tallafa ma wadanda ke cikin tsananin kuncin rayuwa.