Home Labaru Tsaro: Janar Faruk Yahaya Ya Ce Za Su Ji Da ‘Yan Bindiga...

Tsaro: Janar Faruk Yahaya Ya Ce Za Su Ji Da ‘Yan Bindiga Da Yaren Da Su Ke Fahimta

17
0
Janar Faruk Yahaya

Babban Hafsan Sojojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce za a bi da ‘yan bindiga, da masu garkuwa da mutane cikin yaren da su ke fahimta.

Janar Yahaya ya bayyana haka ne, yayin bikin rufe wani taro da ya shirya karo na biyu da na uku a Abuja.

Furucin shugaban sojojin dai ya na zuwa ne, yayin da ake samun karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga a fadin Nijeriya, inda ya ce sojoji na ci-gaba da jajircewa a kan aikin su na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Ya ce ya na so ya yi amfani da wannan damar ya shawarci wadanda ke rura wutar rikicin da ake gani a fadin kasar nan da su daina ayyukan rashin kishin kasa, kamar yadda ya ce sun dage a kan tabbatar da zaman lafiya a kowane bangare na kasar nan cikin lokaci kalilan.