Home Labaru Matsaya: Shugaban Nijeriya Na Gaba Zai Fito Ne Daga Kudu – Gwamnoni

Matsaya: Shugaban Nijeriya Na Gaba Zai Fito Ne Daga Kudu – Gwamnoni

10
0
Southern Gov

Gwamnonin jihohin kudancin Nijeriya 17, sun bayyana goyon bayan su ga hukuncin kotun Jihar Rivers da ya ba jihar damar karbar harajin VAT maimakon gwamnatin tarayya, tare da bukatar ganin shugaban Nijeriya na gaba ya fito daga yankin su.

Matsayin gwamnonin dai ya biyo bayan taron da su ka gudanar a garin Enugu, wanda ya tattauna batutuwa da dama da su ka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma siyasa.

Taron, wanda ya gudana a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya yaba da yadda jihohin yankin kudu ke aiwatar da dokar hana yawon kiwo, yayin da taron ya bukaci jihohin da ba su riga sun amince da dokar hana kiwon ba su gaggauta yin haka.

Haka kuma, taron ya bukaci amfani da jami’an tsaro na shiyya da kuma bukatar tuntuba da hadin kai a tsakanin su, tare da musayar bayanan asiri domin kare lafiyar jama’a da dukiyoyin mazauna yankin su.

Yayin da gwamnonin su ka sake jaddada bukatar su ta sauya fasalin zaman tarayyar da ake amfani da shi yanzu haka a Nijeriya, sun kuma sake bayyana matsayin su na ganin shugaban kasar da za a zaba a shekara ta 2023 ya fito daga kudancin Nijeriya domin tabbatar da adalci ga kowane sashe na kasa.