Home Labaru Tsaro: Janar Buratai Ya Bukaci Karin Kudaden Aiki Domin Yaki Da Boko...

Tsaro: Janar Buratai Ya Bukaci Karin Kudaden Aiki Domin Yaki Da Boko Haram

228
0
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya

Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana bukatar gwamnati ta sake zuba kudade a yakin da Sojoji ke yi da ta’addanci, domin samun damar fuskantar kalubalen tsaro yadda ya kamata.

Buratai ya bayyana haka ne, yayin wani taron horar da jami’an sashen kudi na rundunar Sojin kasa da ya gudana a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Janar Buratai wanda ya samu wakilcin babban kwamanda shiyya ta 6 na rundunar Sojin kasa Jamil Sarham, ya ce rundunar Sojin kasa ta na fama da karancin kudade idan aka duba girman ayyukan tabbatar da tsaron da take yi, da kuma matsalolin tsaron da ke Nijeriya.

Sai dai ya tabbatar da cewa, sabbin tsare-tsare da dokokin da gwamnati ta kirkiro a fannin kudi ya taimaka wajen rage sata da barnatar da kudade a rundunar Sojin.

A karshe Buratai ya yi kira ga Sojoji su tabbatar sun kasance masu biyayya ga gwamnatin Nijeriya, su kuma zama masu biyayya ga dokokin kasa.