Home Labaru Balaguro: Daga Saudiyya Shugaba Buhari Zai Wuce Birnin London

Balaguro: Daga Saudiyya Shugaba Buhari Zai Wuce Birnin London

342
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai wuce birnin London a ranar Asabar mai zuwa, bayan ya kammala abin da ya kai shi kasar Saudiyya.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari zai shafe tsawon makonni biyu a birnin London a wata tafiya ta kashin kan sa.

Adesina, ya ce shugaba Buhari zai bar Nijeriya zuwa kasar Saudiyya domin halartar taron zuba jari karo na uku da kasar ke jagoranta a birnin Riyadh, sannan zai gana da Sarki Salman da Sarki Abdullah na kasar Jordan.

Ya ce a ranar Laraba, shugaba Buhari zai halarci wani taro mai take, ‘Afirka ina muka dosa’a birnin Riyadh, tare da shugabannin kasashen Kenya da Congo-Brazzaville da kuma Burkina Faso.

Bayan ya kammala taron ne, shugaba Buhari zai wuce Birtaniya, inda ake sa ran ya dawo Nijeriya ranar 17 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.