Home Labaru Kasuwanci Sarrafa Kudade: CBN Ya Yi Hadaka Da Masallatai Da Coci-Coci

Sarrafa Kudade: CBN Ya Yi Hadaka Da Masallatai Da Coci-Coci

335
0

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce yayi hadin gwiwa da masallatai da coci-coci don su tallafa wajen koyar da ilimin sarrafa kudade a Najeriya.

Wani darakta a bankin Kofo Salam-Alada,  ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Abuja.

Salam-Alada

 Ya ce Ilimin sarrafa kudade wani ilimi ne da zai koyar da mutum hanyoyi da dubaru akan yadda zai sarrafa kudadenshi, haka zalika zai koyar da mutum yadda zai kula da dukiyar sa ta yadda za ta habbaka har ya kai ga gaci.

Salam-Alada, ya bayyana cewa babban bankin ya shirya gangamin don ya koyar da wasu mabiya addinai ilimin sarrafa kudin ta yadda za su taimaka wajen koyar da ilimin ga sauran mutane.

Ya bayyana cewa babban bankin ya yanke hukuncin yin wannan gangamin duba da yadda mafi yawan yan Najeriya ke da riko da addini.

 A cewarshi, CBN a shirye yake ya yi aiki da duk kungiyar da take da niyyar samar da wajen koyar da ilimin sarrafa kudade da zai taimaka wajen habbaka arzikin Najeriya.