Home Labaru Tsaro: Hukumar DSS Ta Kama Shugaban ‘Yan Bindiga A Kano

Tsaro: Hukumar DSS Ta Kama Shugaban ‘Yan Bindiga A Kano

835
0

Hukumar tsaro ta DSS a jihar Kano, ta kama daya daga cikin masu garkuwa da mutane, kuma shugaba ga ‘yan bindigar da suka kai wa tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa hari.

Mutumin mai suna Muhammad Sani Akazakwai, an cafke shi a gidan mahaifiyarsa dake Kano, a lokacin da yake zaune a gidan yana jinyar ciwon da aka ji masa a lokacin da suka yi artabu da ‘yan sanda.

Hukumar ta bayyanawa manema labarai cewa Sani Akazakwai, ya ce bayan kai wa tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa ya gudo Kano domin ya yi jinyar ciwon da yaji, inda bayan bincike an gano bindigogi guda 50, wanda ya bayyana cewa ya gaje su daga wajen mahaifin sa.

 Shugaban ‘yan bindigar ya ce biyu daga cikin yaransa yanzu haka suna cikin daji da bindigogi guda bakwai da suka kwace a lokacin da suka kashe ‘yan sanda.