Wasu tubabbun ‘yan ta’adda guda hudu sun mika makamansu tare da kayan sojoji ga hukumar ‘yan sandan a jihar Zamfara.
Gwamnatin jihar ta ce wannan babbar nasara ce ta fannin tabbatar da wanzuwar tsaro da daidaito a jihar, inda gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ya nuna farin cikinsa tare da alkawarin yin duk abinda ya dace domin ganin zaman lafiya da lumana ta ci gaba da samuwa a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce makaman da tubabbun suka yada sun hada da bindiga daya mai kirar Ak 47 da wasu kala guda biyu, da alburusai da kuma kayan sojoji.
Ya kara da cewar wannan nasarar ba wai ta cafke ‘yan ta’adda kadai bace, harda yada makamai da ‘yan ta’adda ke yi.
Ya kara da cewa, bayan yarda da ta ginu a tsakanin tubabbun ‘yan ta’addan da kwamitin tabbatar da tsaro, ‘yan ta’addan da kansu ke daukar mataki akan ‘yan uwansu da suka yi musa taurin kai, suka ki rungumar zaman lafiya.
A watan Yuni shekara ta 2019 wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka ajiye makamai, inda wasu kuma suka ajiye makamansu a watan Augusta.